25 Yesu ya kira su ya ce musu, “Kun sani sarakunan al'ummai sukan nuna musu iko, hakimansu ma sukan gasa musu iko.
26 Ba haka zai zama a tsakaninku ba. Amma duk wanda yake son zama babba a cikinku, lalle ne ya zama baranku.
27 Wanda duk kuma yake so ya shugabance ku, lalle ne ya zama bawanku,
28 kamar yadda Ɗan Mutum ma ya zo ba domin a bauta masa ba sai dai domin shi ya yi bautar, yă kuma ba da ransa fansa saboda mutane da yawa.”
29 Suna fita daga Yariko ke nan, sai wani babban taro ya bi shi.
30 Ga mutum biyu makafi zaune a bakin hanya. Da suka ji dai Yesu ne yake wucewa, sai suka ɗaga murya suka ce, “Ya Ubangiji, ka ji tausayinmu, ya Ɗan Dawuda!”
31 Jama'a suka kwaɓe su su yi shiru. Amma sai ƙara ɗaga murya suke yi ƙwarai da gaske, suna cewa, “Ya Ubangiji, ka yi mana jinƙai, ya Ɗan Dawuda!”