29 Suna fita daga Yariko ke nan, sai wani babban taro ya bi shi.
30 Ga mutum biyu makafi zaune a bakin hanya. Da suka ji dai Yesu ne yake wucewa, sai suka ɗaga murya suka ce, “Ya Ubangiji, ka ji tausayinmu, ya Ɗan Dawuda!”
31 Jama'a suka kwaɓe su su yi shiru. Amma sai ƙara ɗaga murya suke yi ƙwarai da gaske, suna cewa, “Ya Ubangiji, ka yi mana jinƙai, ya Ɗan Dawuda!”
32 Sai Yesu ya tsaya, ya yi kiransu ya ce, “Me kuke so in yi muku?”
33 Suka ce masa, “Ya Ubangiji, mu dai mu sami gani!”
34 Domin tausayi, sai Yesu ya taɓa idanunsu, nan take suka gani, suka bi shi.