8 Da magariba ta yi, mai garkar inabin ya ce wa wakilinsa, ‘Kirawo ma'aikatan, ka biya su hakkinsu, ka fara daga na ƙarshe har zuwa na farko.’
9 Da waɗanda aka ɗauka wajen la'asar suka zo, sai ko wannensu ya sami dinari guda.
10 To, da na farkon suka zo suka zaci za su sami fiye da haka. Amma su ma aka ba ko wannensu dinari guda.
11 Da suka karɓa sai suka yi ta yi wa maigidan gunaguni,
12 suna cewa, ‘Na bayan nan, ai, aikin sa'a guda kawai suka yi, ka kuwa daidaita mu, mu da muka yini zubur muna shan wahala da zafin rana.’
13 Sai ya amsa wa ɗayansu ya ce, ‘Abokina, ai, ban cuce ka ba. Ashe, ba mu yi lada da kai a kan dinari guda ba?
14 Sai ka karɓi halalinka ka tafi. Ni ne na ga damar ba waɗannan na ƙarshe daidai da yadda na ba ka.