14 Sai makafi da guragu suka zo wurinsa a Haikalin, ya kuwa warkar da su.
15 Amma manyan firistoci da malaman Attaura suka ga abubuwan al'ajabi da ya yi, har yara suna sowa a Haikalin suna cewa, “Hosanna ga Ɗan Dawuda!” sai suka ji haushi.
16 Suka ce masa, “Kana jin abin da waɗannan suke faɗa?” Yesu kuwa ya ce musu, “I. Amma ba ku taɓa karantawa ba cewa,‘Kai ne ka shiryar da 'yan yara da masu shan mama su yabe ka’?”
17 Sai ya bar su, ya fita daga birnin, ya tafi Betanya, ya sauka a can.
18 Kashegari da sassafe yana komowa birni, sai ya ji yunwa.
19 Da ya ga wani ɓaure a gefen hanya, ya je wurin, amma bai sami kome ba, sai ganye kawai. Sai ya ce wa ɓauren, “Kada ka ƙara yin 'ya'ya har abada!” Nan take ɓauren ya bushe.
20 Da almajiran suka ga haka, suka yi mamaki suka ce, “Yaya ɓauren nan ya bushe haka nan da nan?”