21 Suka ce, “Na Kaisar ne.” Sa'an nan ya ce musu, “To, sai ku ba Kaisar abin da yake na Kaisar, ku kuma ba Allah abin da yake na Allah.”
22 Da suka ji haka, sai suka yi mamaki, suka rabu da shi, suka yi tafiyarsu.
23 A ran nan sai waɗansu Sadukiyawa (su da suke cewa, ba tashin matattu) suka zo wurinsa, suka yi masa tambaya,
24 suka ce, “Malam, Musa dai ya ce, ‘In mutum ya mutu, bai bar na baya ba, sai lalle ɗan'uwansa ya auri matar, ya haifa wa ɗan'uwansa 'ya'ya.’
25 To, an yi waɗansu 'yan'uwa maza bakwai a cikinmu. Na farkon ya yi aure, da ya rasu, da yake bai haifu kuma ba, sai ya bar wa ɗan'uwansa matarsa.
26 Haka ya faru ga na biyun da na ukun, har ya kai kan na bakwai ɗin.
27 Bayansu duka sai matar ta rasu.