31 “Sa'ad da Ɗan Mutum ya zo cikin ɗaukakarsa tare da mala'iku duka, sa'an nan ne zai zauna a maɗaukakin kursiyinsa.
32 Za a tara dukan al'ummai a gabansa, zai kuma ware su dabam dabam, kamar yadda makiyayi yake ware tumaki da awaki.
33 Zai sa tumaki a damansa, awaki kuwa a hagunsa.
34 Sa'an nan ne Sarki zai ce wa waɗanda suke dama da shi, ‘Ku zo, ya ku da Ubana ya yi wa albarka, sai ku gāji mulkin da aka tanadar muku tun daga farkon duniya.
35 Domin na ji yunwa, kun ba ni abinci. Na ji ƙishirwa, kun ba ni na sha. Na yi baƙunci, kun saukar da ni.
36 Na yi huntanci, kun tufasar da ni. Na yi rashin lafiya, kun ziyarce ni. Ina kurkuku, kun kula da ni.’
37 Sa'an nan ne masu adalci za su amsa masa su ce, ‘Ya Ubangiji, a yaushe muka gan ka da yunwa muka cishe ka, ko kuwa da ƙishirwa muka shayar da kai?