43 Na yi baƙunci, ba ku sauke ni ba. Na yi huntanci, ba ku tufasar da ni ba. Na yi rashin lafiya, ina kuma kurkuku, ba ku kula da ni ba.’
44 Sa'an nan su ma za su amsa su ce, ‘Ya Ubangiji, a yaushe muka gan ka da yunwa, ko da ƙishirwa, ko da baƙunci, ko da huntanci, ko da rashin lafiya, ko a kurkuku, ba mu kula da kai ba?’
45 Sa'an nan zai amsa musu ya ce, ‘Hakika, ina gaya muku, tun da yake ba ku yi wa ɗaya daga cikin waɗannan mafi ƙanƙanta ba, ai, ni ne ba ku yi mini ba.’
46 Waɗannan ne za su shiga madawwamiyar azaba, masu adalci kuwa rai madawwami.”