72 Sai ya sāke musawa har da rantsuwa ya ce, “Ban ma san mutumin nan ba.”
73 Jim kaɗan sai na tsaitsayen suka matso, suka ce wa Bitrus, “Lalle kai ma ɗayansu ne, don irin maganarka ta tona ka.”
74 Sai ya fara la'anar kansa, yana ta rantse-rantse, yana cewa, “Ban ma san mutumin nan ba.” Nan da nan sai zakara ya yi cara.
75 Sai Bitrus ya tuna da maganar Yesu cewa, “Kafin carar zakara za ka yi musun sanina sau uku.” Sai ya fita waje, ya yi ta rusa kuka.