25 Sai duk jama'a suka amsa suka ce, “Alhakin jininsa a wuyanmu, mu da 'ya'yanmu!”
26 Sa'an nan ya sakar musu Barabbas. Bayan ya yi wa Yesu bulala, sai ya ba da shi a gicciye shi.
27 Sai sojan mai mulki suka kai Yesu cikin fadar mai mulki, suka tara dukan ƙungiyar soja a kansa.
28 Sai suka tuɓe shi, suka yafa masa wata jar alkyabba.
29 Suka yi wani rawani na ƙaya, suka sa masa a kā, suka danƙa masa sanda a hannunsa na dama, suka kuma durƙusa a gabansa, suna yi masa ba'a suna cewa, “Ranka ya daɗe, Sarkin Yahudawa!”
30 Suka tattofa masa yau, suka karɓe sandan, suka ƙwala masa a ka.
31 Da suka gama yi masa ba'a, sai suka yaye masa alkyabbar, suka sa masa nasa tufafi, suka tafi da shi su gicciye shi.