7 Sai Yesu ya ce masa, “A rubuce yake kuma cewa, ‘Kada ka gwada Ubangiji Allahnka.’ ”
8 Har wa yau dai, sai Iblis ya kai shi kan wani dutse mai tsawo ƙwarai, ya nunnuna masa dukan mulkokin duniya da ɗaukakarsu.
9 Ya kuma ce masa, “Duk waɗannan zan ba ka in ka faɗi a gabana ka yi mini sujada.”
10 Sai Yesu ya ce masa, “Tafi daga nan, kai Shaiɗan! domin a rubuce yake cewa,‘Kă yi wa Ubangiji Allahnka sujada,Shi kaɗai za ka bauta wa.’ ”
11 Sa'an nan Iblis ya rabu da shi. Sai ga mala'iku sun zo suna yi masa hidima.
12 To, da Yesu ya ji an tsare Yahaya, sai ya tashi zuwa ƙasar Galili.
13 Ya kuma bar Nazarat, ya koma Kafarnahum da zama, can bakin teku, a kan iyakar ƙasar Zabaluna da Naftali,