1 Da Yesu ya ga taro masu yawa sai ya hau dutse. Da ya zauna, almajiransa kuma suka zo gunsa.
2 Sai ya buɗe baki ya koya musu.
3 “Albarka tā tabbata ga waɗanda suka san talaucinsu na ruhu, domin Mulkin Sama nasu ne.
4 “Albarka tā tabbata ga masu nadāma, domin za a sanyaya musu rai.
5 “Albarka tā tabbata ga masu tawali'u, domin za su gāji duniya.