4 Ko kuwa yaya za ka iya ce wa ɗan'wanka, ‘Bari in cire maka ɗan hakin daga idonka,’ alhali kuwa da gungume a naka ido?
5 Kai munafuki! Sai ka fara cire gungumen da yake idonka tukuna, sa'an nan ka gani sosai yadda za ka cire ɗan hakin daga idon ɗan'uwanka.
6 “Kada ku ba karnuka abin da yake tsattsarka. Kada kuma ku jefa wa alhanzir lu'ulu'unku, don kada su tattake su, su juyo su kyakketa ku.”
7 “Ku yi ta roƙo, za a ba ku. Ku yi ta nema, za ku samu. Ku yi ta ƙwanƙwasawa, za a kuwa buɗe muku.
8 Duk wanda ya roƙa, akan ba shi, mai nema yana tare da samu. Wanda ya ƙwanƙwasa kuma za a buɗe masa.
9 To, wane ne a cikinku, ɗansa zai roƙe shi gurasa, ya ba shi dutse?
10 Ko kuwa ya roƙe shi kifi, ya ba shi maciji?