28 Da ya shiga wani gida sai makafin suka zo gare shi. Yesu ya ce musu, “Kun gaskata ina da ikon yin haka?” Sai suka ce masa, “I, ya Ubangiji!”
29 Sa'an nan ya taɓa idanunsu, ya ce, “Yă zama muku gwargwadon bangaskiyarku.”
30 Sai idanunsu suka buɗe. Amma Yesu ya kwaɓe su ƙwarai, ya ce, “Kada fa kowa ya ji labarin.”
31 Amma suka tafi suka yi ta baza labarinsa a duk ƙasar.
32 Sun tashi ke nan, sai aka kawo masa wani bebe mai aljan.
33 Bayan an fitar da aljanin, sai beben ya yi magana, taron kuwa suka yi mamaki, suka ce, “Kai! Ba a taɓa ganin irin wannan a cikin Isra'ila ba.”
34 Amma sai Farisiyawa suka ce, “Ai, da ikon sarkin aljannu yake fitar da aljannu.”