4 Yesu kuwa, da yake ya san tunaninsu, ya ce, “Don me kuke mugun tunani a zuciyarku?
5 Wanne ya fi sauƙi, a ce, ‘An gafarta maka zunubanka,’ ko kuwa a ce, ‘Tashi ka yi tafiya’?
6 Amma domin ku sakankance Ɗan Mutum yana da ikon gafarta zunubi a duniya”–sai ya ce wa shanyayyen–“Tashi, ka ɗauki shimfiɗarka ka tafi gida.”
7 Shi kuwa ya tashi ya tafi gida.
8 Da taron suka ga haka, sai tsoro ya kama su, suka ɗaukaka Allah, wanda ya ba mutane iko haka.
9 Da Yesu ya yi gaba, ya ga wani mutum mai suna Matiyu a zaune, yana aiki a wurin karɓar haraji. Ya ce masa, “Bi ni.” Sai ya tashi ya bi shi.
10 Sa'ad da kuwa Yesu yake cin abinci a gida, sai ga masu karɓar haraji da masu zunubi da yawa sun zo, sun zauna tare da shi da almajiransa.