23 Ko su ma, in dai ba su nace wa rashin bangaskiyarsu ba, sai a ɗaura aure da su, domin Allah yana da ikon sāke mai da su.
24 Kai ma da aka saro daga zaitun ɗin da asalinsa yake na jeji, aka ɗaura aure da kai a jikin zaitun ɗin na gida, saɓanin yadda aka saba, balle waɗannan rassa na asali, da za a ɗaura aure da su a jikin zaitun ɗin nan nasu na asali?
25 'Yan'uwa, ga wata asirtacciyar gaskiya da nake so ku sani, domin kada ku zaci ku masu hikima ne, taurarewar nan–wadda ba mai tabbata ba ce–ta sami Isra'ilawa ne, har adadin al'ummai masu ɗungumawa zuwa ga Allah ya cika.
26 Ta haka nan ne Isra'ila duka za su sami ceto, kamar yadda yake a rubuce cewa,“Mai Ceto zai zo daga Sihiyona,Zai kuma kawar da rashin bin Allah daga zuriyar Yakubu,”
27 “Cikar alkawarina a gare su ke nan,Sa'ad da na ɗauke musu zunubansu.”
28 A game da bishara kuma, maƙiyan Allah ne su, domin amfaninku ne kuwa. Amma a game da zaɓen Allah, su ƙaunatattunsa ne, albarkacin kakannin kakanninsu.
29 Domin baiwar Allah da kiransa ba sa tashi.