Rom 6 HAU

Mutuwa ga Zunubi, Rayuwa ga Almasihu

1 To, me kuma za mu ce? Ma ci gaba da yin zunubi ne domin alherin Allah yă haɓaka?

2 A'a, ko kusa! Mu da muka mutu ga zunubi, ƙaƙa za mu ƙara rayuwa a cikinsa har yanzu?

3 Ashe, ba ku sani ba duk ɗaukacinmu da aka yi wa baftisma a cikin Almasihu Yesu, a cikin mutuwarsa aka yi mana baftismar ba?

4 Saboda haka, an binne mu da shi ke nan, ta wurin baftisma cikin mutuwarsa, domin kamar yadda aka ta da Almasihu daga matattu ta wurin ɗaukakar Uba, haka mu ma mu yi zaman sabuwar rayuwa.

5 Tun da yake mun zama ɗaya da shi wajen kwatancin mutuwarsa, ashe kuwa, za mu zama ɗaya ma a wajen tashinsa.

6 Wato, mun sani an gicciye halayenmu na dā tare da shi, domin a hallakar da ikon nan namu mai zunnubi, kada mu ƙara bauta wa zunubi.

7 Wanda ya yi irin wannan mutuwa kuwa, an kuɓutar da shi daga zunubi ke nan.

8 Amma idan muka mutu tare da Almasihu, mun gaskata za mu rayu tare da shi kuma.

9 Mun sani tun da yake an ta da Almasihu daga matattu, ba zai sāke mutuwa ba ke nan, mutuwa ba ta da sauran wani iko a kansa.

10 Mutuwar nan da ya yi kuwa, ya mutu ne sau ɗaya tak ba ƙari, saboda shafe zunubanmu, amma rayuwar da yake yi, yana rayuwa ne, rayuwa ga Allah.

11 Haka ku ma sai ku lasafta kanku kamar ku matattu ne ga zunubi, amma kuna a raye rayuwa ga Allah, ta wurin Almasihu Yesu.

12 Saboda haka, kada ku yarda zunubi yă mallaki jikin nan naku mai mutuwa har da za ku biye wa muguwar sha'awarsa.

13 Kada kuma ku miƙa gaɓoɓinku su zama kayan aikin mugunta, don yin zunubi. Amma ku miƙa kanku ga Allah, kamar waɗanda aka raya bayan mutuwa, kuna miƙa gaɓoɓinku ga Allah kayan aikin adalci.

14 Domin zunubi ba zai mallake ku ba, tun da yake ba shari'a take iko da ku ba alherin Allah ne.

Bayin Adalci

15 To, ƙaƙa? Wato, sai mu yi zunubi don shari'a ba ta iko da mu, sai alherin Allah? A'a, ko kusa!

16 Ba ku sani ba, shi wanda kuke miƙa kanku a gare shi domin yi wa biyayya, lalle ku bayi ne na wanda kuke yi wa biyayya ɗin (ko bautar zunubi wanda ƙarshensa mutuwa ne, ko bautar biyayya wadda ƙarshenta adalci ce)?

17 Amma godiya tā tabbata ga Allah, ko da yake dā can ku bayin zunubi ne, a yanzu kam kuna biyayya da zuciya ɗaya ga irin koyarwar nan da aka yi muku.

18 Da aka 'yanta ku kuma daga bautar zunubi, kun zama bayin aikin adalci.

19 Mai da magana nake yi irin ta yau da kullum, saboda rarraunar ɗabi'arku. Wato, kamar yadda dā can kuka miƙa gaɓoɓinku ga bautar rashin tsarki, da mugun aiki a kan mugun aiki, haka kuma a yanzu sai ku miƙa gaɓoɓinku ga bautar aikin adalci, domin aikata tsarkakan ayyuka.

20 Sa'ad da kuke bayin zunubi, ba ruwanku da aikin adalci.

21 To, wace fa'ida kuka samu a lokacin nan, a game da aikin da kuke jin kunya a yanzu? Lalle ƙarshen irin wannan aiki mutuwa ne.

22 Amma a yanzu da aka 'yanta ku daga bautar zunubi, kun zama bayin Allah, sakamakonku shi ne tsarkakewa, ƙarshenta kuwa rai madawwami ne.

23 Gama sakamakon zunubi mutuwa ne, amma baiwar Allah ita ce rai madawwami a cikin Almasihu Yesu Ubangijinmu.

Surori

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13