26 Ta haka nan ne Isra'ila duka za su sami ceto, kamar yadda yake a rubuce cewa,“Mai Ceto zai zo daga Sihiyona,Zai kuma kawar da rashin bin Allah daga zuriyar Yakubu,”
27 “Cikar alkawarina a gare su ke nan,Sa'ad da na ɗauke musu zunubansu.”
28 A game da bishara kuma, maƙiyan Allah ne su, domin amfaninku ne kuwa. Amma a game da zaɓen Allah, su ƙaunatattunsa ne, albarkacin kakannin kakanninsu.
29 Domin baiwar Allah da kiransa ba sa tashi.
30 Kamar yadda kuka ƙi bin Allah a dā, amma a yanzu aka yi muku jinƙai saboda rashin biyayyarsu,
31 haka su ma da suke marasa biyayya a yanzu, yanzu a yi musu jinƙai kamar yadda aka yi muku.
32 Don Allah ya kulle kowa a cikin rashin biyayya, domin ya nuna jinƙai ga kowa.