4 Amma me Allah ya amsa masa? Cewa ya yi, “Na keɓe wa kaina mutum dubu bakwai waɗanda ba su taɓa durƙusa wa Ba'al ba.”
5 Haka ma a wannan zamani akwai ragowa, waɗanda aka zaɓa saboda alherinsa.
6 In kuwa na alheri ne, ba sauran cewa ya dogara ga aikin lada ke nan. In ba haka ba, ashe, alheri ba alheri ba ne kuma.
7 To, yaya ke nan? Ashe, abin da Isra'ila take nema, ba su samu ba ke nan, amma zaɓaɓɓun nan sun samu, sauran kuwa sun taurare.
8 Yadda yake a rubuce cewa,“Allah ya toshe musu basira,Ya ba su ido, ba na gani ba,Da kuma kunne, ba na ji ba,Har ya zuwa yau.”
9 Dawuda kuma ya ce,“Da ma shagalinsu ya zama musu tarko, abin shammatarsu,Sanadin faɗuwarsu kuma, har aniyarsu ta koma kansu.
10 Idonsu kuma yă shiga duhu, har su kasa gani,Ka kuma tanƙwara bayansu har abada.”