11 Kada ku sassauta a wajen himma, ku himmantu a ruhu, kuna bauta wa Ubangiji.
12 Sa zuciyar nan taku ta sa ku farin ciki, ku jure wa wahala, ku nace wa yin addu'a.
13 Ku agaji tsarkaka, ku himmantu ga yi wa baƙi alheri.
14 Ku sa wa masu tsananta muku albarka. Ku sa musu albarka, kada ku la'ance su.
15 Ku taya masu farin ciki farin ciki, masu kuka kuwa ku taya su kuka.
16 Ku yi zaman lafiya da juna. Kada ku nuna alfarma, sai dai ku miƙa kanku ga aikata ayyukan tawali'u. Kada ku aza kanku masu hikima ne.
17 Kada ku rama muguntar kowa da mugunta. Ku yi ta lura al'amuranku su zama daidai a gaban kowa.