14 Ku sa wa masu tsananta muku albarka. Ku sa musu albarka, kada ku la'ance su.
15 Ku taya masu farin ciki farin ciki, masu kuka kuwa ku taya su kuka.
16 Ku yi zaman lafiya da juna. Kada ku nuna alfarma, sai dai ku miƙa kanku ga aikata ayyukan tawali'u. Kada ku aza kanku masu hikima ne.
17 Kada ku rama muguntar kowa da mugunta. Ku yi ta lura al'amuranku su zama daidai a gaban kowa.
18 In mai yiwuwa ne, a gare ku, ku yi zaman lafiya da kowa.
19 Ya ku ƙaunatattuna, kada ku ku yi ramuwa, sai dai ku bar wa fushin Allah. Domin a rubuce yake cewa, “Ramuwa tawa ce, ni zan saka, in ji Ubangiji.”
20 Har ma “in maƙiyinka yana jin yunwa, sai ka ci da shi. In yana jin ƙishirwa, ka shayar da shi. Don ta haka ne za ka tula garwashin wuta a kansa.”