10 Kamar yadda yake a rubuce cewa,“Babu wani mai adalci, babu, ko ɗaya,
11 Babu wani mai fahimta, babu wani mai neman Allah.
12 Duk sun bauɗe, sun zama marasa amfani baki ɗaya,Babu wani mai aiki nagari, babu kam, ko da guda ɗaya.”
13 “Maƙogwaronsu kamar buɗaɗɗen kabari ne,Maganarsu ta yaudara ce.”“Masu ciwon baki ne.”
14 “Yawan zage-zage da ɗacin baki gare su.”
15 “Masu hanzarin zub da jini ne,
16 Ta ko'ina suka bi sai hallaka da baƙin ciki,