1 To, da yake mu kuɓutattu ne ta wurin bangaskiya, muna da salama ke nan a gun Allah, ta wurin Ubangijinmu Yesu Almasihu.
2 Ta wurinsa kuma muka sami shiga alherin nan da muke a ciki, saboda bangaskiyarmu, muna kuma taƙama da sa zuciyarmu ga samun ɗaukakar nan ta Allah.
3 Banda haka ma, har muna taƙama da shan wuyarmu, da yake mun sani shan wuya take sa jimiri,
4 jimiri kuma yake sa ingataccen hali, ingataccen hali kuma yake sa sa zuciya,
5 ita sa zuciyar nan kuwa ba ta sāce iska faufau, domin Allah ya kwarara ƙaunarsa a zukatanmu, ta wurin Ruhu Mai Tsarki da aka ba mu.
6 Tun muna raunana tukuna, Almasihu ya mutu a daidaitaccen lokaci, domin marasa bin Allah.