1 Saboda haka a yanzu, ba sauran kayarwa ga waɗanda suke na Almasihu Yesu.
2 Ka'idar nan ta Ruhu mai ba da rai da yake ga Almasihu Yesu ta 'yanta ni daga ka'idar zunubi da ta mutuwa.
3 Abin da ba shi yiwuwa Shari'a ta yi domin ta kasa saboda halin ɗan adam, Allah ya yi shi, wato ya ka da zunubi a cikin jiki, da ya aiko da Ɗansa da kamannin jikin nan namu mai zunubi, domin kawar da zunubi.
4 Wannan kuwa domin a cika hakkokin Shari'a ne a gare mu, mu da ba zaman halin mutuntaka muke yi ba, sai dai na Ruhu.