3 Abin da ba shi yiwuwa Shari'a ta yi domin ta kasa saboda halin ɗan adam, Allah ya yi shi, wato ya ka da zunubi a cikin jiki, da ya aiko da Ɗansa da kamannin jikin nan namu mai zunubi, domin kawar da zunubi.
4 Wannan kuwa domin a cika hakkokin Shari'a ne a gare mu, mu da ba zaman halin mutuntaka muke yi ba, sai dai na Ruhu.
5 Masu zaman halin mutuntaka, ai, ƙwallafa ransu ga al'amuran halin mutuntaka suke yi, masu zaman Ruhu kuwa ga al'amuran Ruhu.
6 Ƙwallafa rai ga al'amuran halin mutuntaka ƙarshensa mutuwa ne, ƙwallafa rai ga ala'muran Ruhu kuwa rai ne da salama.
7 Don ƙwallafa rai ga al'amuran halin mutuntaka gāba ne da Allah, gama ba ya bin Shari'ar Allah, ba kuwa zai iya ba.
8 Masu zaman halin mutuntaka, ba dama su faranta wa Allah rai.
9 Amma ku kam, ba masu zaman halin mutuntaka ba ne, masu zaman Ruhu ne, in dai har Ruhun Allah yana zaune a zuciyarku. Duk wanda ba shi da Ruhun Almasihu kuwa, ba na Almasihu ba ne.