17 Don a Nassi an ce da Fir'auna, “Na girmama ka ne musamman, domin in nuna ikona a kanka, domin kuma a sanar da sunana a duniya duka.”
18 Wato, yana nuna jinƙai ga wanda ya so, yana kuma taurara zuciyar wanda ya so.
19 Kila ka ce mini, “To, don me har yanzu yake ganin laifi? Wa zai iya tsayayya da nufinsa?”
20 Ya kai ɗan adam! Wane ne kai har da za ka yi jayayya da Allah? Ashe, abin da aka gina zai iya ce wa magininsa, “Don me ka yi ni haka?”
21 Ashe, maginin tukwane ba ya iko da yumɓu, ya gina wata domin aiki mai martaba, wata kuma don kasasshen aiki, duk daga curi ɗaya?
22 To, ƙaƙa fa? Allah da yake yana so ya nuna fushinsa, ya kuma bayyana ikonsa, sai ya haƙura matuƙar haƙuri da waɗanda suka cancanci fushinsa, suka kuma isa hallaka,
23 Nufinsa ne yă bayyana yalwar ɗaukakarsa ga waɗanda ya yi wa jinƙai, wato, waɗanda dā ma ya yi wa tanadin ɗaukaka?