9 Alkawarin kuwa shi ne, “Baɗi war haka zan dawo, Saratu kuma za ta haifi ɗa.”
10 Banda haka ma, sa'ad da Rifkatu ta yi ciki da mutumin nan ɗaya, wato, kakanmu Ishaku,
11 tun ba ta haifi 'ya'yan ba, balle su yi wani abu mai kyau ko marar kyau–don nufin Allah bisa ga zaɓensa ya tabbata, ba ga aikin lada ba, sai dai ga kiransa–
12 aka ce mata, “Wan zai bauta wa ƙanen.”
13 Kamar yadda yake a rubuce cewa, “Yakubu na so, Isuwa na ƙi.”
14 To, me kuma za mu ce? Allah ya yi rashin adalci ke nan? a'a, ko kusa!
15 Domin ya ce wa Musa, “Wanda zan yi wa jinƙai, zan yi masa jinƙan, wanda zan nuna wa tausayi kuwa, zan nuna masa tausayin.”