4 Amma sa'ad da alherin Allah Mai Cetonmu da ƙaunarsa ga 'yan adam suka bayyana,
5 sai ya cece mu, ba don wani aikin adalci da mu muka yi ba, a'a, sai dai domin jinƙan nan nasa, albarkacin wankan nan na sāke haihuwa, da kuma sabuntawar nan ta Ruhu Mai Tsarki,
6 wanda ya zubo mana a yalwace ta wurin Yesu Almasihu Mai Cetonmu.
7 Wannan kuwa domin a kuɓutar da mu bisa ga alherinsa ne, mu kuma zama magāda masu bege ga rai madawwami.
8 Maganar nan tabbatacciya ce.Ina so ka ƙarfafa waɗannan abubuwa ƙwarai, don waɗanda suka ba da gaskiya ga Allah su himmantu ga aiki nagari, waɗannan abubuwa kuwa masu kyau ne, masu amfani kuma ga mutane.
9 Amma ka yi nesa da gardandamin banza, da ƙididdigar asali, da husuma, da jayayya a kan Shari'a, domin ba su da wata riba, aikin banza ne kuma.
10 Mutumin da yake sa tsattsaguwa kuwa, in ya ƙi kula da gargaɗinka na farko da na biyu, to, sai ka fita sha'aninsa.