4 har suka yi wa macijin nan sujada, don shi ne ya bai wa dabbar ikonsa, suka kuma yi wa dabbar sujada, suna cewa, “Wa ya yi kama da dabbar nan? Wa kuma zai iya yaƙi da ita?”
5 An kuwa ba dabbar nan baki, tana fariya da maganganun saɓo, aka kuma yardar mata ta zartar da iko, har wata arba'in da biyu.
6 Sai ta buɗe bakinta don ta saɓi Allah, ta yi ta saɓon sunansa, da wurin zamansa, da waɗanda suke a zaune a Sama.
7 Aka kuma yardar mata ta yaƙi tsarkaka, ta cinye su. Aka kuma ba ta iko a kan kowace kabila, da jama'a, da harshe, da al'umma.
8 Duk mazaunan duniya kuma, za su yi mata sujada, wato, duk wanda, tun farkon duniya, ba a rubuta sunansa a Littafin Rai na Ɗan Ragon nan da yake Yankakke ba.
9 Duk mai kunnen ji, yă ji.
10 Kowa aka ƙaddara wa bauta, sai ya je aikin bautar.Kowa kuwa ya yi kisa da takobi, to, kuwa da takobi za a kashe shi lalle.Wannan yana nuna jimiri da bangaskiya na tsarkaka.