1 Bayan wannan na ga mala'iku huɗu, a tsaye a kusurwa huɗu ta duniya, suna tsare da iskokin nan huɗu na duniya, don kada wata iska ta busa a kan ƙasa, ko a kan teku, ko a kan wani itace.
2 Sai na ga wani mala'ika yana hawa daga mafitar rana, riƙe da hatimin Allah Rayayye. Sai ya yi wa mala'ikun nan huɗu magana da murya mai ƙarfi, waɗanda aka bai wa ikon azabtar da ƙasa da teku,
3 yana cewa, “Kada ku azabtar da ƙasa, ko teku, ko itatuwa, sai mun buga wa bayin Allahnmu hatimi a goshinsu tukuna.”
4 Sai na ji adadin waɗanda aka buga wa hatimin, dubu ɗari da arba'in da huɗu ne, daga kowace kabilar Isra'ila,
5 wato, an yi wa dubu goma sha biyu hatimi daga kabilar Yahuza, dubu goma sha biyu daga kabilar Ra'ubainu, dubu goma sha biyu daga kabilar Gad,
6 dubu goma sha biyu daga kabilar Ashiru, dubu goma sha biyu daga kabilar Naftali, dubu goma sha biyu daga kabilar Manassa,
7 dubu goma sha biyu daga kabilar Saminu, dubu goma sha biyu daga kabilar Lawi, dubu goma sha biyu daga kabilar Issaka,
8 dubu goma sha biyu daga kabilar Zabaluna, dubu goma sha biyu daga kabilar Yusufu, dubu goma sha biyu kuma daga kabilar Biliyaminu.
9 Bayan wannan na duba, ga wani ƙasaitaccen taro, wanda ya fi gaban ƙirge, daga kowace al'umma, da kabila, da jama'a, da harshe, suna a tsaitsaye a gaban kursiyin, a gaban Ɗan Ragon kuma, a saye da fararen riguna, da gazarin dabino a hannunsu,
10 suna ta da murya da ƙarfi suna cewa, “Yin ceto ya tabbata ga Allahnmu wanda yake a zaune a kan kursiyin, da kuma Ɗan Rago!”
11 Dukan mala'iku kuwa suna tsaitsaye a kewaye da kursiyin, da dattawan nan, da kuma rayayyun halittan nan guda huɗu, suka fāɗi a gaban kursiyin suka yi wa Allah sujada,
12 suna cewa, “Hakika! Yabo, da ɗaukaka, da hikima, da godiya, da girma, da iko, da ƙarfi su tabbata ga Allahnmu har abada abadin! Amin! Amin!”
13 Sai ɗaya daga cikin dattawan nan ya yi mini magana, ya ce, “Su wane ne waɗannan da suke a saye da fararen riguna, daga ina kuma suke?”
14 Sai na ce masa, “Ya shugaba, ai, ka sani.” Sai ya ce mini, “Su ne waɗanda suka fito daga matsananciyar wahala, sun wanke rigunansu, suka mai da su farare da jinin Ɗan Ragon nan.
15 Saboda haka ne suke a gaban kursiyin Allah, suna bauta masa dare da rana a Haikalinsa. Na zaune a kan kursiyin nan kuwa, zai kare su da Zatinsa,
16 ba za su ƙara jin yunwa ba, ba kuma za su ƙara jin ƙishirwa ba, ba za su ƙara jin zafin rana ko ƙuna ba sam,
17 domin Ɗan Ragon nan da yake a tsakiyar kursiyin, shi zai zama makiyayinsu, zai kuwa kai su maɓuɓɓugar ruwan rai. Allah kuma zai share musu dukan hawaye.”