7 Aka kuma yardar mata ta yaƙi tsarkaka, ta cinye su. Aka kuma ba ta iko a kan kowace kabila, da jama'a, da harshe, da al'umma.
8 Duk mazaunan duniya kuma, za su yi mata sujada, wato, duk wanda, tun farkon duniya, ba a rubuta sunansa a Littafin Rai na Ɗan Ragon nan da yake Yankakke ba.
9 Duk mai kunnen ji, yă ji.
10 Kowa aka ƙaddara wa bauta, sai ya je aikin bautar.Kowa kuwa ya yi kisa da takobi, to, kuwa da takobi za a kashe shi lalle.Wannan yana nuna jimiri da bangaskiya na tsarkaka.
11 Sa'an nan na ga wata dabba na fitowa daga cikin ƙasa. Tana da ƙaho biyu kamar na ɗan rago, maganarta kuwa kamar ta macijin nan.
12 Tana zartar da duk ikon dabbar nan ta farko, a kan idonta, tana kuma sa duniya da duk mazauna a cikinta, su yi wa dabbar nan ta farko sujada, wadda aka warkar mata da rauninta mai kamar na ajali.
13 Tana yin manyan abubuwan al'ajabi, har ma tana sa wuta ta zuba a ƙasa daga sama, a gaban idon mutane.