2 ta tsakiyar hanyar birnin kuma, ta kowane gefen kogin, akwai itatuwan rai masu haihuwar 'ya'ya iri goma sha biyu, kowane wata suna haihuwa, ganyen itatuwan kuwa saboda lafiyar al'ummai ne.
3 Ba sauran wani abin la'antarwa, amma kursiyin Allah, shi da Ɗan Rago, zai kasance a cikinsa. Bayinsa za su bauta masa,
4 za su kuma ga fuskarsa, sunansa kuwa zai kasance a goshinsu.
5 Ba za a ƙara yin dare ba, ba za su bukaci hasken fitila, ko na rana ba, domin Ubangiji Allah zai haskaka su, za su kuma sha ni'imar Mulki har abada abadin.
6 Sai ya ce mini, “Wannan magana tabbatacciya ce, ta gaskiya ce kuma. Ubangiji, Allahn ruhohin annabawa ya aiko mala'ikansa, ya nuna wa bayinsa abin da lalle ne zai auku ba da daɗewa ba.”
7 “Ga shi kuwa, ina zuwa da wuri. Albarka tā tabbata ga wanda yake kiyaye maganar annabcin littafin nan.”
8 Ni Yahaya, ni ne na ji, na kuma ga waɗannan abubuwa. Sa'ad da kuwa na ji su, na kuma gan su, sai na fāɗi a gaban mala'ikan da ya nuna mini su, domin in yi masa sujada.