1 Bayan wannan na duba, sai ga wata ƙofa a buɗe a Sama. Muryar farko da na ji dā, mai kama da ƙaho, ta ce mini, “Hawo nan, zan nuna maka abin da lalle ne ya auku bayan wannan.”
2 Nan da nan kuwa Ruhu ya iza ni, sai ga wani kursiyi a girke a Sama, da wani a zaune a kai.
3 Na zaunen kuwa ya yi kama da yasfa da yakutu. Kewaye da kursiyin kuma akwai wani bakan gizo mai kama da zumurrudu.
4 Kewaye da kursiyin kuwa akwai waɗansu kursiyai ashirin da huɗu, da dattawa ashirin da huɗu a zaune a kai, masu fararen tufafi, da kuma kambin zinariya a kansu.