1 A hannun dama na wanda yake zaune a kursiyin kuma, sai na ga wani littafi rubutacce ciki da bai, an yimƙe shi da hatimi bakwai.
2 Na kuma ga wani ƙaƙƙarfan mala'ika, yana shela da murya mai ƙarfi cewa, “Wa ya cancanta ya buɗe littafin nan, ya kuma ɓamɓare hatimansa?”
3 Ba kuwa wani a Sama ko a ƙasa, ko a ƙarƙashin ƙasa, da zai iya buɗe littafin, balle yă duba a cikinsa.
4 Sai na yi ta kuka da ba a sami wanda ya cancanta ya buɗe littafin, ko ya duba a cikinsa ba, ko ɗaya.