1 Wani mutum ne ya yi rashin lafiya, sunansa Li'azaru na Betanya, ƙauyen su Maryamu da 'yar'uwarta Marta.
2 Maryamun nan kuwa, wadda ɗan'uwanta Li'azaru ba shi da lafiya, ita ce wadda ta shafa wa Ubangiji man ƙanshi, ta kuma shafe ƙafafunsa da gashinta.
3 To, 'yan'uwan nan mata suka aika masa, suka ce, “Ya Ubangiji, ga shi, wanda kake ƙaunan nan ba shi da lafiya.”
4 Da Yesu ya ji haka ya ce, “Wannan rashin lafiya, ƙarshensa ba mutuwa ba ne, domin a ɗaukaka Allah ne, a kuma ɗaukaka Ɗan Allah ta wurinsa.”
5 Yesu kuwa na ƙaunar Marta da 'yar'uwarta, da kuma Li'azaru.
6 To, da ya ji Li'azaru ba shi da lafiya, sai ya ƙara kwana biyu.
7 Bayan haka ya ce wa almajiran, “Mu koma ƙasar Yahudiya.”