15 Ina kuwa farin ciki da ba na nan, saboda ku domin ku ba da gaskiya. Amma mu dai je wurinsa.”
16 Sai Toma, wanda ake kira Ɗan Tagwai, ya ce wa 'yan'uwansa almajirai, “Mu ma mu tafi, mu mutu tare da shi.”
17 Da Yesu ya isa, ya tarar Li'azaru, har ya kwana huɗu a kabari.
18 Betanya kuwa kusa da Urushalima take, misalin mil biyu.
19 Yahudawa da yawa sun zo su yi wa Marta da Maryamu ta'aziyyar ɗan'uwansu.
20 Da jin Yesu na zuwa, sai Marta ta je taryensa, Maryamu kuwa ta zauna a gida.
21 Sai Marta ta ce wa Yesu, “Ya Ubangiji, da kana nan da ɗan'uwana bai mutu ba.