24 Marta ta ce masa, “Na sani zai tashi a tashin matattu a ranar ƙarshe.”
25 Yesu ya ce mata, “Ai, ni ne tashin matattu, ni ne kuma rai. Wanda ya gaskata da ni, ko ya mutu zai rayu.
26 Wanda kuwa yake raye, yake kuma gaskatawa da ni, ba zai mutu ba har abada. Kin gaskata wannan?”
27 Ta ce masa, “I, ya Ubangiji. Na gaskata kai ne Almasihu, Ɗan Allah, shi wannan mai zuwa duniya.”
28 Da ta faɗi haka, ta je ta kirawo 'yar'uwa tata Maryamu, ta raɗa mata ta ce, “Ga Malam ya zo, yana kiranki.”
29 Ita kuwa da jin haka, ta yi maza ta tashi ta nufi wurinsa.
30 Yesu dai bai iso ƙauyen ba tukuna, har yanzu yana wurin da Marta ta tarye shi.