32 Da Maryamu ta iso inda Yesu yake, ta gan shi, sai ta faɗi a gabansa ta ce masa, “Ya Ubangiji, da kana nan da dan'uwana bai mutu ba.”
33 Da Yesu ya ga tana kuka, Yahudawan da suka zo tare da ita su ma, suna kuka, sai ya nisa a ransa, ya yi juyayi gaya.
34 Ya kuma ce, “Ina kuka sa shi?” Suka ce masa, “Ya Ubangiji, zo ka gani.”
35 Sai Yesu ya yi hawaye.
36 Don haka Yahudawa suka ce, “Dubi yadda yake ƙaunarsa!”
37 Amma waɗansunsu suka ce, “Ashe, wanda ya buɗe wa makahon nan ido, ba zai iya hana wannan mutum mutuwa ba?”
38 Sai Yesu ya sāke nisawa a ransa, ya iso kabarin. Kabarin kuwa kogon dutse ne, da wani dutse kuma an rufe bakin.