9 Yesu ya amsa ya ce, “Ba sa'a goma sha biyu ce yini ɗaya ba? Kowa yake tafiya da rana ba ya tuntuɓe, don yana ganin hasken duniyan nan.
10 Amma kowa yake tafiya da dare yakan yi tuntuɓe, don ba haske a gare shi!”
11 Ya faɗi haka, sa'an nan ya ƙara ce musu, “Amininmu Li'azaru ya yi barci, amma za ni in tashe shi.”
12 Sai almajiran suka ce masa, “Ya Ubangiji, in dai barci ne ya ɗauke shi, ai, zai warke.”
13 Alhali kuwa, Yesu zancen mutuwar Li'azaru yake, amma su sun ɗauka yana nufin barcin hutawa ne.
14 Sai Yesu ya gaya musu a fili, ya ce, “Li'azaru dai ya mutu.
15 Ina kuwa farin ciki da ba na nan, saboda ku domin ku ba da gaskiya. Amma mu dai je wurinsa.”