1 Idin Ƙetarewa sauran kwana shida, sai Yesu ya zo Betanya inda Li'azaru yake, wanda Yesu ya tasa daga matattu.
2 Nan aka yi masa abincin dare, Marta ce ta yi hidima, Li'azaru kuwa yana cikin masu ci tare da shi.
3 Sai Maryamu ta ɗauko awo guda na man ƙanshi na nardi tsantsa, mai tamanin gaske, ta shafa a ƙafafun Yesu, sa'an nan ta shafe su da gashinta. Duk gidan ya game da ƙanshin man.
4 Amma Yahuza Iskariyoti, ɗaya daga cikin almajiransa, wato wanda zai bāshe shi, ya ce,