27 “Yanzu ina jin nauyi a raina. Me zan ce kuwa? In ce, ‘Ya Uba ka ɗauke mini wannan lokaci’? A'a, ai, dā ma na zo ne takanas domin wannan lokaci.
28 Ya Uba, ka ɗaukaka sunanka.” Sai aka ji wata murya daga Sama ta ce, “Na riga na ɗaukaka shi, zan kuma ƙara ɗaukaka shi,”
29 Da taron da yake tsaye a wurin suka ji muryar, suka ce, “An yi cida.” Waɗansu kuwa suka ce, “Wani mala'ika ne ya yi masa magana.”
30 Yesu ya amsa ya ce, “Ba saboda ni aka yi wannan muryan nan ba, sai dominku.
31 Yanzu ne za a yi wa duniyan nan shari'a, yanzu ne kuma za a tuɓe mai mulkin duniyan nan.
32 Ni kuwa bayan an ɗaga ni daga ƙasa zan ja dukan mutane gare ni.”
33 Ta faɗar haka ya kwatanta irin mutuwar da zai yi.