30 Yesu ya amsa ya ce, “Ba saboda ni aka yi wannan muryan nan ba, sai dominku.
31 Yanzu ne za a yi wa duniyan nan shari'a, yanzu ne kuma za a tuɓe mai mulkin duniyan nan.
32 Ni kuwa bayan an ɗaga ni daga ƙasa zan ja dukan mutane gare ni.”
33 Ta faɗar haka ya kwatanta irin mutuwar da zai yi.
34 Sai taron suka amsa masa suka ce, “Shari'armu ta gaya mana, cewa Almasihu zai tabbata har abada. To, yaya za ka ce lalle ne a ɗaga Ɗan Mutum? Wane ne Ɗan Mutum ɗin?”
35 Yesu ya ce musu, “Haske na tare da ku har ɗan lokaci kaɗan na gaba. Ku yi tafiya tun haske na tare da ku, kada duhu ya ci muku. Mai tafiya a cikin duhu bai san inda yake tafiya ba.
36 Ku gaskata da hasken, tun kuna tare da shi, domin ku zama mutanen haske.”Yesu ya faɗi haka, sa'an nan ya tafi ya ɓuya musu.