33 Ta faɗar haka ya kwatanta irin mutuwar da zai yi.
34 Sai taron suka amsa masa suka ce, “Shari'armu ta gaya mana, cewa Almasihu zai tabbata har abada. To, yaya za ka ce lalle ne a ɗaga Ɗan Mutum? Wane ne Ɗan Mutum ɗin?”
35 Yesu ya ce musu, “Haske na tare da ku har ɗan lokaci kaɗan na gaba. Ku yi tafiya tun haske na tare da ku, kada duhu ya ci muku. Mai tafiya a cikin duhu bai san inda yake tafiya ba.
36 Ku gaskata da hasken, tun kuna tare da shi, domin ku zama mutanen haske.”Yesu ya faɗi haka, sa'an nan ya tafi ya ɓuya musu.
37 Amma ko da yake ya sha yin mu'ujizai da yawa a gabansu, duk da haka, ba su gaskata shi ba,
38 domin a cika faɗar Annabi Ishaya cewa,“Ya Ubangiji, wa ya gaskata jawabinmu?Ga wa kuma aka bayyana ikon Ubangiji?”
39 Shi ya sa ba su iya ba da gaskiya ba. Domin Ishaya ya sāke cewa,