20 Lalle hakika, ina gaya muku, wanda ya yi na'am da duk wanda na aiko, ya yi na'am da ni ke nan. Wanda ya yi na'am da ni kuwa, to, ya yi na'am da wanda ya aiko ni.”
21 Bayan da Yesu ya faɗi haka, ya ji nauyi a ransa, ya yi shaida ya ce, “Lalle hakika, ina gaya muku, ɗayanku zai bāshe ni.”
22 Sai almajiran suka duddubi juna, suka rasa da wanda yake.
23 Wani daga cikin almajiransa kuwa, wanda Yesu yake ƙauna, yana kishingiɗe gab da Yesu.
24 Sai Bitrus ya alamta masa ya ce, “Gaya mana, da wa yake?”
25 Shi kuwa da yake kishingiɗe haka gab da Yesu ya karkata, ya ce masa, “Ya Ubangiji, wane ne?”
26 Sai Yesu ya amsa ya ce, “Shi ne wanda zan tsoma 'yar lomar nan in ba shi.” Da ya tsoma 'yar lomar kuwa, sai ya ba Yahuza, Ɗan Saminu Iskariyoti.