17 Sai waɗansu almajiransa suka ce wa juna, “Me yake nufi da ce mana, ‘Bayan ɗan lokaci kaɗan ba za ku gan ni ba, bayan ɗan lokaci kaɗan kuma za ku gan ni’? da kuma cewa, ‘Domin za ni wurin Uba’?”
18 Suka ce, “Me yake nufi da, ‘Bayan ɗan lokaci kaɗan ’ ɗin? Ai, ba mu san abin da yake faɗa ba.”
19 Yesu kuwa ya sani suna so su tambaye shi, sai ya ce musu, “Wato kuna tambayar juna ne abin da nake nufi da cewa, ‘Bayan ɗan lokaci kaɗan ba za ku gan ni ba, bayan ɗan lokaci kaɗan kuma za ku gan ni’?
20 Lalle hakika, ina gaya muku, za ku yi kuka da kuma gunji, amma duniya za ta yi farin ciki. Za ku yi baƙin ciki, amma baƙin cikinku zai koma farin ciki.
21 Idan mace tana naƙuda takan sha wuya, don lokacin haihuwarta ya yi. Amma da zarar ta haifi jinjirin, ba ta ƙara tunawa da wahalar da ta sha, domin murnar an sami baƙon duniya.
22 Haka ku ma yanzu kuke tare da baƙin ciki, amma zan sāke ganinku, sa'an nan zuciyarku za ta yi fari, ba kuwa mai ɗauke muku farin cikinku.
23 A ran nan, ba za ku yi mini wata tambaya ba. Lalle hakika, ina gaya muku, kome kuka roƙi Uba zai ba ku saboda sunana.