1 Da Yesu ya faɗi haka, sai ya ɗaga kai sama ya ce, “Ya Uba, lokaci ya yi. Ka ɗaukaka Ɗanka domin Ɗan ya ɗaukaka ka,
2 tun da ka ba shi iko a kan dukkan 'yan adam, yă ba da rai madawwami ga duk waɗanda ka ba shi.
3 Rai madawwami kuwa, shi ne su san ka, Allah Makaɗaici na gaskiya, da kuma Yesu Almasihu da ka aiko.
4 Na ɗaukaka ka a duniya da yake na cika aikin da ka ba ni in yi.
5 Yanzu kuma, ya Uba, ka ɗaukaka ni zuwa ga zatinka da ɗaukakan nan da nake da ita tare da kai tun kafin duniya ta kasance.