27 Sai Bitrus ya sāke yin musu. Nan da nan kuwa zakara ya yi cara.
28 Daga wurin Kayafa kuma suka kai Yesu fādar mai mulki. Da asuba ne kuwa. Su kansu ba su shiga fādar ba, wai don kada su ƙazantu su kāsa cin jibin Ƙetarewa.
29 Saboda haka, Bilatus ya fito wajensu, ya ce, “Wace ƙara kuka kawo ta mutumin nan?”
30 Sai suka amsa masa suka ce, “Da wannan ba mai laifi ba ne, ai, da ba mu bāshe shi gare ka ba.”
31 Bilatus ya ce musu, “Ku tafi da shi da kanku mana, ku hukunta shi bisa ga shari'arku!” Sai Yahudawa suka ce masa, “Ai, ba mu da ikon zartar da hukuncin kisa a kan kowa.”
32 Wannan kuwa don a cika maganar da Yesu ya yi ne, wadda ta kwatanta irin mutuwar da zai yi.
33 Sai Bilatus ya koma cikin fāda, ya kira Yesu ya ce masa, “Ashe, kai ɗin nan, kai ne Sarkin Yahudawa?”