27 Sa'an nan ya ce wa almajirin, “Ga tsohuwarka nan!” Tun daga wannan lokaci fa almajirin nan ya kai ta gidansa.
28 Bayan haka, Yesu da ya san duk an gama kome, domin a cika Nassi sai ya ce, “Ina jin ƙishirwa.”
29 To, akwai wani gora cike da ruwan tsami a ajiye a nan. Sai suka jiƙa soso da ruwan tsamin, suka soka a sandan izob suka kai bakinsa.
30 Da Yesu ya tsotsi ruwan tsamin nan ya ce, “An gama!” Sa'an nan ya sunkuyar da kansa ya ba da ransa.
31 Da yake ran nan ranar shiri ce, don kada a bar jikuna a gicciye ran Asabar (domin wannan Asabar ɗin babbar rana ce), sai Yahudawa suka roƙi Bilatus a karya ƙafafunsu, a kuma ɗauke jikunan.
32 Sai soja suka zo suka karya ƙafafun na farkon nan, da kuma na ɗayan da aka gicciye tare da shi.
33 Amma da suka zo wurin Yesu, suka kuma ga ya riga ya mutu, ba su karya ƙafafunsa ba.