12 sai ta ga mala'iku biyu saye da fararen tufafi a zaune inda dā gawar Yesu take, ɗaga wajen kai, ɗaya kuwa wajen ƙafafu.
13 Suka ce mata, “Uwargida, don me kike kuka?” Ta ce musu, “Ai, an ɗauke Ubangijina, ban kuwa san inda aka sa shi ba.”
14 Da ta faɗi haka sai ta juya ta ga Yesu tsaye, amma ba ta gane Yesu ne ba.
15 Yesu ya ce mata, “Uwargida, don me kike kuka? Wa kuma kike nema?” Saboda kuma ta zaci shi ne mai aikin lambun, ta ce masa, “Maigida, in kai ne ka ɗauke shi, gaya mini inda ka sa shi mana, ni kuwa in ɗauke shi.”
16 Yesu ya ce mata, “Maryamu!” Sai ta juya ta ce masa da Yahudanci, “Rabboni!” wato Malam.
17 Yesu ya ce mata, “Kada ki riƙe ni, domin har yanzu ban hau wurin Uba ba tukuna. Sai dai ki tafi wurin 'yan'uwana ki ce musu ina hawa wurin Ubana kuma Ubanku, Allahna kuma Allahnku.”
18 Sai Maryamu Magadaliya ta je ta ce wa almajiran, “Na ga Ubangiji!” Ta kuma ce shi ya faɗa mata waɗannan abubuwa.