9 Don kafin lokacin nan ba su fahimci Nassin nan ba, cewa lalle ne yă tashi daga matattu.
10 Sai almajiran suka koma gida.
11 Maryamu kuwa tana tsaye a bakin kabarin daga waje, tana kuka. Tana cikin kuka sai ta duƙa, ta leƙa kabarin,
12 sai ta ga mala'iku biyu saye da fararen tufafi a zaune inda dā gawar Yesu take, ɗaga wajen kai, ɗaya kuwa wajen ƙafafu.
13 Suka ce mata, “Uwargida, don me kike kuka?” Ta ce musu, “Ai, an ɗauke Ubangijina, ban kuwa san inda aka sa shi ba.”
14 Da ta faɗi haka sai ta juya ta ga Yesu tsaye, amma ba ta gane Yesu ne ba.
15 Yesu ya ce mata, “Uwargida, don me kike kuka? Wa kuma kike nema?” Saboda kuma ta zaci shi ne mai aikin lambun, ta ce masa, “Maigida, in kai ne ka ɗauke shi, gaya mini inda ka sa shi mana, ni kuwa in ɗauke shi.”