1 Bayan haka Yesu ya sāke bayyana kansa ga almajiran a bakin Tekun Tibariya. Ga kuwa yadda ya bayyana kansa.
2 Bitrus, da Toma wanda ake kira Ɗan Tagwai, da Nata'ala na Kana ta ƙasar Galili, da 'ya'yan nan na Zabadi, da kuma waɗansu almajiransa biyu, duk suna nan tare,
3 Sai Bitrus ya ce musu, “Za ni su.” Suka ce masa, “Mu ma mā tafi tare da kai.” Sai suka fita suka shiga jirgi. Amma a daren nan ba su kama kome ba.
4 Gari na wayewa sai ga Yesu tsaye a bakin gaci, amma almajiran ba su gane Yesu ne ba.